14 Oktoba 2014 - 15:17

A cikin wani tsarin ta na ci gaban fannin ma'adunai, Gwamanatin Nijar ta sanarda raraba wasu lasisin neman ma'adunai karkashin kasa ga wasu kanfanonin ciki da wajen kasar 12.

Gwamnatin ta bayarada wannan sanarwa yayin taron ministocin ta na makon jiya kuma yankunan nemen ma'adunan da suka hada da zinare, azurfa, gawayi da dai sauran su a jihohin Tillabery dake yammacin kasar, da jihar Tawa dake tsakiya da kuma  Agades dake Arewacin kasar.   A cikin yajejenoyoyin da gwamnatin ta sa hannu da wadanan kanfanonin an kiyasta kasar zata anfana da kudade da yawan su ya kai sama da milliyan 35 na dallar Amurka a shekara uku masu zuwa.    Baya ga dai wadanan ma'adunan Allah ya albarkaci Nijar da arzikin kashen Urenium wace ake hasashen a shekaru masu zuwa zata kasance ta uku a duniya wajen arzikin uranium, to saidai duk kwa da wannan kasar na zamen kura baya cikin kasahen mafi talaici a Duniya. ABNA